26 Afirilu 2015 - 18:34
An yi Allah wadai da Saudiya a Nigeria

Mabiya Ahlul-Baiti{a.s} a Nigeria sunyi tofin Allah wadai akan harin da kasar Saudiya ke kaiwa akan Yemen

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a,s}-abna-duban mutane ne suka fito a garin Kano dage arewacin Nigeria domin yin zanga-zangar yin Allah wadai da harin fin karfi da kasar Saudiya ke kaiwa akan al’ummar Yemen.

Masu zanga-zanga sun bukaci dakatar da kai hare-hare akan fararen hula da yara kanana da kuma rusa wurare masu muhimmanci na kasar Yemen wanda Saudiya ke yi.

Masu zanga-zangar na dauke da kwalayen da a ka rubuta Allah wadai da Saudiya kuma suna kira da a hukunta shuwugabannin kasar Saudiya.

Ayau ma haka kasar Saudiya ta kai hare-hare a wasu yan kuna na kasra Yemen inda harin yai sanadiyar rasa rayukan mutane da dama.ABNA